
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana cewa, wadanda ke bashi kyauta a shekarun da suka gabata a yanzu sune ke neman ya tallafa musu.
Peter Obi ya bayyana hakane a wajan taron Jam’iyyar Labour party din da ya wakana a Abuja.
Yace zasu shiga zabe me zuwa a shirye kuma zasu tsayar da mutane na gari a matsayin ‘yan takara.
Peter Obi ya kara da cewa, matsin tattalin arziki yayi tsanani ta yada wanda a baya suke gayyatarsa yana cin abinci tare dasu amma yanzu sune ke neman ya taimaka musu.