Wednesday, October 14
Shadow

Wani shaida a shari’ar Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi zargin cewa, Tsohon Gwamnan ya ware dala $600,000 dan bayar da cin hanci ga EFCC

Jami’in hukumar hana rashawa da cin hanci, EFCC Segun Kayode wanda ya bayar da shaida a gaban babbar kotun jihar Kaduna, game da shari’ar tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

Yace El-Rufai bisa hadin kai da dansa, Bashir El-Rufai da wani Lauya, AU Mustapha (SAN) da kuma wani me suna Jimi Lawal ne suka hada wannan lamari.

Segun Kayode ya kawo sautin murya na wayar da El-Rufai yayi game da maganar a zaman kotun na ranar Talata wanda aka kwashe kusan awanni 8 ana sauraro.

Shaidar yace El-Rufai na shirin kulle kamfanin Singularity dan kaucewa binciken da EFCC kewa Kamfanin.

A yanzu dai Kotun ta daga Shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba da 1 ga watan Nuwamba.

Karanta Wannan  SUBHANULLAH: Yanzu-Yanzu wata Motar Sumfuri ta gwamnatin jihar Sokoto ta samu mummunan hatsari a garin Zariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *