
Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta nemi a samu wasu su shiga tsakani kan rikicin dake faruwa tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti.
Shugaban kungiyar reshen Arewa da Abuja, Rev. John Joseph Hayab ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai,.
Yace ‘yan Najeriya na kallon ‘yan majalisar da mutunci kada su bari lamarin ya canja.
Yace kamata yayi a yi kokarin kare mutuncin ‘yan majalisar dama ‘yan Najeriya baki daya.