
Tauraruwar fina-finan Kudu, Doris Ogala ta bayyana cewa,Pastor Chris Okafo ya aikata Alfasha da ita kuma ta ji dadi, ya gamsar da ita.
Tace dalilin haka ma har ta rabu da mijinta bisa zummar cewa zai aureta.
Tace kwatsam sai gashi taga Bidiyo da hotunan aurensa sun bayyana.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyon data wallafa a shafinta na sada zumunta inda aka ganta tana ta sharbar kuka.