
Kakakin jam’iyyar PDP a jihar Legas, Hakeem Amode ya koma jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakane a wata ganawa da manema labarai tare da masoyansa a Ikeja ranar Litinin.
Sun bayyana cewa, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Abdul-Azeez Adediran (Jandor), da ya koma APC ne ya dauki hankulansu suka koma jam’iyyar APC.
A jawabinsa yace duka jam’iyyar PDP a jihar daga sama har kasa sun koma APC inda yace saboda jam’iyyar PDP ta tasa alkibla.