Najeriya ta zama kasa ta 3 a Duniya wajan yawan cin bashi daga bankin Duniya a karkashin mulkin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.
A shekarar 2024 kadai, Gwamnatin Najeriya ta ciwo bashin jimullar Dala biliyan 2.2 daga bankin na Duniya.
A baya dai kamin zuwan gwamnatin Tinubu, Najeriyarce kasa ta 4 a cikin jerin kasashen da suka fi cin bashin bankin Duniyar.
Kasar Bangladesh ce dai ta daya a Duniya wajan yawan cin bashin daga bankin Duniya, Sai kuma kasar Pakistan ta 2.