Monday, September 28
Shadow

Wata Sabuwa: Wasu Rahotanni na bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin sayen kamfanin Sadarwa na MTN

Wani Rahoto daga Sahara Reporters na cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin zama wanda ke da mafi yawan hannun jari a kamfanin sadarwa na MTN.

Rahotan yace Shugaban zai sayi hannun jarinne ta hannun kamfanin Mafab Communications da IHS Towers.

Sannan kuma shugaban Kamfanin MTN, Karl Olutokun Toriola ne zai saukaka kasuwancin.

Sahara Reporters dai sun ce wata majiya ce daga bangaren harkar sadarwa ta sanar dasu hakan.

Saidai ba’a bayyana hannun jarin na nawa shugaba Tinubu zai siya ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Na hadu da wani Saurayi yace yana sona, Har na amince sai na ganshi da Hular APC nan take nace ban sonsa>>Inji Wannan Budurwar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *