Wednesday, January 15
Shadow

Ya ake gane mace ‘yar iska

Ana gane mace ‘yar iska ce ta hanyoyin dabi’u da shigar jikinta ko kalamai da kuma irin mutanen da take ma’amala dasu.

Mace wadda take ‘yar iska, ko ace ”yar bariki, takan kasance Mara kunya ta yanda zata iya fadar komai ko yin komai ba tare da Shakkar kowa ba.

Mace ”yar iska zaka ji kalamanta bata tsaftace su, takan iya fadar kalaman batsa ko na zagi ko cin mutunci ga kowa.

Hakanan takan kasance idan tana magana da namiji zata iya kallon sa ido cikin ido ba tare da shakka ba.

Hakanan mace ”yar iska, bata damu ba Dan namiji ya taba jikinta ba, ba zata taba yin korafi ba Dan namiji ya taba jikinta ba, asali ma zata iya yin gaisuwa, runguma, ko sumbatar namiji a bainar jama’a ba tare da damuwa ba.

Karanta Wannan  Wacece mace mai kyau

Hakanan mace ”yar iska zaka ga abokanta ko kawayenta ‘yan iska ne, da wuya ta rika yin ma’amala da mutanen kirki.

Mace ”yar iska zaka ga takan yi shigar banza, ko dai ta saka kaya masu matseta da nuna Surar jikinta ko kuma ta saka kaya masu sharara wanda zaka iya hango cikin jikinta, ko kuma ta saka kaya wanda basu rufe duka jikinta ba ta yanda za’a iya ganin saman nonuwanta ko tsakiyar nonuwanta da sauransu.

Mace ”yar iska zaka ga bata damu da yin ibada ba ko yin ma’amala me kyauba.

Mace ”yar iska zata iya aikata zina Dan Neman kudi ko kuma da sunan soyayya.

Karanta Wannan  Kaikayin Azzakari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *