Tuesday, March 18
Shadow

‘Yan Najeriya, Ghana, China, da India ne suka bace aka rasa inda suke bayan da suka shiga kasar Canada da cewar sun je yin karatune

Wani rahoto ya bayyana cewa akalla dalibai dubu 50 ne suka bace aka rasa inda suke bayan da suka shiga kasar Canada da sunan yin karatu.

Daiban sun fito ne daga kasashen Duniya daban-daban wa da suka hada da kasar India da dalibai 19,582 suka shiga kasar ta Canada amma suka ki zuwa su yi rijistar fara karatu aka rasa inda suke, me biye mata itace kasar China dake da dalibai 4,279 da suma bayan shiga kasar Canada da sunan karatu suka bace, kasa ta uku itace Najeriya dake da dalibai 3,902 wanda suma sun shiga kasar Canada da sunan yin karatu amma sun bace, kasa ta gaba itace kasar Ghana itama dalibanta sun isa kasar Canada da sunan yin karatu amma suka bace.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan Katuwar Doyar da ba'a taba ganin me girmanta ba da aka noma a Jos, Jihar Filato

Daliban dai sun shiga kasar Canada ne a tsakanin watannin Maris zuwa Afrilu.

Rahoton yace wasu daliban yaudararsu aka yi inda wasu kuma da gangan suka aikata hakan dan su samu shiga kasar ta canada

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *