Hukumar ‘yansandan Najeriya ta sanar da cewa ta dakile yunkurin garkuwa da mutane a karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina inda ta kubutar da mutane 21.
Kakakin ‘yansandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitr ga manema labarai inda yace sun samu wannan nasara ne a aikin da suka yi tare da sojoji da kuma ‘yan Bijilante.
Yace sun dakile yunkurin garkuwa da mutanen ne a Ka’ida, Unguwar One Boy, da Danmarke quarters duka a Jibia ranar 7 ga watan Nuwamba.
Yacw maharan sun kai harinne inda su kuma suka kai dauki cikin gaggawa inda aka shafe awa guda ana bata kashi.
Yace ‘yan Bindigar sun tsere daga wajan ba shiri.
Yace sun kubutar da mutane 16 saidai 5 daga ciki sun samu raunukan bindiga.
Yace jami’in Bijilante daya da jami’in hukumar tsaro mallakin jihar ta Katsina sun samu raunuka.