
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya bayyana Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a matsayin wanda ya jahilci lamarin matsalar tsaron Najeriya.
Sanata ali Ndume na martanine a gidan Talabijin na Arise TV ga barazanar shugaban kasar Amurka, Donald Trump ta kawowa Najeriya hari saboda kashe wadanda ya kira ‘yan ta’adda masu kashe Kiristoci.
Sanata Ali Ndume yace matsalar tsaron Najeriya an kwashe kusan shekaru 16 ana fama da ita kuma ta taba kowane addini, ya danganta da inda lamarin ya faru.
Yace Trump ya jahilci matsalar ne shiyasa yake wannan magana.