Shugaba Bola Tinubu, a yau Talata ya ce shugabannin Afirka za su ci gaba da jajircewa wajen fitar da al’ummarsu daga kangin talauci da gina tattalin arzikinsu a matakan da su ka dace.
Tinubu, wanda ya kasance babban bako na musamman, ya bayyana haka ne a wajen rantsar da shugaba John Mahama a birnin Accra na kasar Ghana.
“Ba mu da wani abin da za mu tabbatar wa kowa sai kanmu. Mun sami hanya mai mahimmanci don samun nasarar mu. Za mu fitar da al’ummarmu daga kangin talauci, mu gina tattalin arziki mai dorewa a kan kan mu.
“A yau, na zo nan ba kawai a matsayina na shugaban Najeriya ba, har ma a matsayina na dan Afirka mai cikakken goyon baya ga Ghana da mutanenta,” in ji Tinubu