Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci.
Ministan kimiyya da fasaha, Chief Uche Geoffrey Nnaji ne ya bayyana haka.
Ya bayyana cewa, za’a saka kirkire-kirkiren da matasa ke yi a gida Najeriya cikin abubuwan da za’a rika kallo a matsayin abin afanarwa ga ‘yan kasa.
Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro na musamman.
Yace tattalin arziki na habakane idan aka ta’allakashi akan kirkire-kirkire da fasaha.