Monday, April 21
Shadow

Zan bayyana fitattun mutune bakwai da na taɓa soyayya da su a Najeriya – Bobrisky

Shahararren ɗan daudun nan, Bobrisky, ya bayyana cewa ya taɓa yin soyayya da fitattun mutane bakwai a Najeriya a cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta.

Bobrisky, wanda aka san shi da halayensa masu jan hankali da faɗin albarkacin bakinsa, ya yi wannan bayani ne yayin da yake bayani kan cin amana da suka tilasta masa ficewa daga ƙasar.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa Bobrisky ya kuma yi alkawarin fallasa sunayen waɗanda ya ke magana a kansu, yana mai kwatanta su da “munafukai” a cikin masana’antar nishadi ta Najeriya.

“Lokaci yana zuwa da zan bayyana sunayen fitattun mutune bakwai da na taɓa yin soyayya da su a Najeriya. Lokaci yana zuwa da zan fallasa munafukai a wannan ƙasa”, in ji shi.

Karanta Wannan  Sunayen Larabawa masu dadi

A cikin bidiyon, Bobrisky ya yi nazari kan suka da ya fuskanta daga wasu shahararrun ‘yan Najeriya da ‘yan siyasa yayin da ya ke fuskantar matsala da Hukumar EFCC.

Ya nuna takaicinsa game da yadda Najeriya ta ƙi amincewa da ainihin halayensa, yana mai cewa ko da zai yi shekara 100 a ƙasar, ba za a taɓa amincewa da shi a matsayin mace a takardu na hukuma ba.

“Ban taɓa sanin cewa ina da muhimmanci sosai ba sai bara, lokacin da ministoci da ‘yan majalisa suka fara tattauna magana a Kai na. Ka yi tunanin minista yana barin aikinsa don ya mai da hankali kan Bobrisky. Shin ina da wannan muhimmanci haka?

Karanta Wannan  Bankin Duniya yace Tattalin arzikin Najeriya zai karu da kaso 3.6

“Ko da zan yi shekara 100 a Najeriya, ba za su taɓa saka ‘mace’ a kan fasfo ko lasisin tuki na ba. Amma a nan, ana girmama ni bisa yadda nake”, in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *