Friday, December 6
Shadow

Ɓangarori uku da Saudiyya ta yi alƙawarin taimaka wa Najeriya

Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed Bin Salman ya yi alkawarin cewa gwamnatin ƙasar za ta taimaka wa Najeriya wajen inganta tattalin arzikinta.

Yarima Bn Salman ya bayar da tabbacin ne bayan ganawa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu a gefen taron ƙasashen Larabawa da Musulmi a birnin Riyadh, wanda aka kammala ranar Litinin.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Mohammed ya yaba da irin tsare-tsaren farfaɗo da tattalin arziki da Tinubu yake ɗauka, inda ya ce irinsu Saudiyya ta ɗauka domin samun ci gaba lokacin da ya zama firaminista.

An shafe kimanin shekara ɗaya ana tattaunawa tsakanin Najeriya da Saudiyya kan batun zuba jarin tun bayan da aka kaddamar da kwamitin kula da harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen.

Shugaba Tinubu ya koma Najeriya a yammacin Talata bayan kammala taron na kwana ɗaya, wanda aka yi bisa haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar ƙasashen Musulmi ta Organization of Islamic Cooperation, da kuma Arab League ta Larabawa.

Aikin gona

Wani ɓangare mai muhimmanci a tattalin arzikin Najeriya shi ne na aikin gona. Ƙasar tana iya noma abubuwa da dama, kuma ɓangaren na ci gaba da samun bunƙasa.

Karanta Wannan  Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà

A baya-bayan nan ne ma Shugaba Tinubu ya kafa ma’aikatar kula da haɓaka kiwon dabbobi ta ƙasa.

Ya ce idan Najeriya na son cin gajiyar kiwon dabbobin da take yi dole ne ta yi yunƙurin magance matsalolin da ɓangaren ke fuskanta na tsawon shekaru.

Gwamnatin Saudiyyar dai ta yi alkawarin cewa za ta tallafa wa Najeriya a harkar noma da kuma ta kiwon dabbobi domin bunƙasa tattalin arzikinta.

Kamfanin kula da harkokin noma da kiwo da kuma zuba jari na Saudiyya (SALIC) ya zuba jarin dala biliyan 1.24 a 2022, a cewra sanarwar da Onanuga ya fitar, domin sayen hannun jari da ya kai kashi 35.43 cikin 100 na kamfanin Olam Agri, ɗaya daga cikin kamfanonin kula da aikin gona na Najeriya.

An kuma tattauna domin ganin cewa kamfanin na Saudiyya ya samu ƙarin hannun jari a Najeriya, sannan Saudiyyar na fatan zuba jarin zai saka kamfanin Olam na Najeriya ya zama sahun gaba a harkokin kasuwanci da suka jiɓanci noma a duniya.

Ɓukatar Saudiyya wajen ganin ta taimka wa Najeriya a ɓangaren zai taimaka matuka, musamman a daidai lokacin da Najeriya ke faɗi-tashin tsayawa da ƙafarta wajen noma abincin da ake ci a cikin gida.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Bidiyo: Yanda matasan turawa 50 a kasar Denmark suka shiga addinin Musulunci

Man fetur da iskar gas

Ɓangaren man fetur da iskar gas, shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin ƙasashen biyu – musamman Najeriya.

Najeriya ce ƙasa mafi arzikin man fetur a nahiyar Afirka, kuma ita ce ta fi kowace ƙasa a nahiyar fitar da man zuwa kasuwar duniya. Sai dai duk da haka ƙasar na fama da ƙaranci da kuma tsadarsa.

Ko a baya-bayan nan ma, an yi ta samun ƙarin farashin fetur a ƙasar tun bayan da Tinubu ya sanar da janye tallafin mai lokacin jawabin kama aiki a watan Mayun 2023.

Dalilin haka ne Saudiyya ta ce za ta ƙara taimaka wa ƙasar don ganin ɓangaren na mai ya ɗore da kuma samun ci gaba.

Ko a bara ma, Saudiyyar ta ɗauki alwashin tallafa wa Najeriya don ganin ta farfaɗo da matatun man ƙasar da zimmar inganta yanayin samar da mai.

“Duk da cewa Najeriya ta mayar da hankali wajen samar da man fetur a tsawon shekaru, sai dai yunkurin gyara matatun ƙasar ya ci tura, abin da ya sa take ci gaba da dogaro kan shigo da shi daga waje.

Karanta Wannan  CBN ta kori manyan jami'an bankin NIRSAL Bank

“Hakan ne ya sa muke so mu taimaka mata,” in ji yariman Saudiyya Mohamed Bn Salman.

Zuba jari da ababen more rayuwa

Har wa yau, ta Saudiyya ta ce tana da burin taimaka wa Najeriya a harkar zuba jari domin inganta harkokin kasuwanci.

Haka kuma Najeriya na son ƙulla alaƙar kasuwanci da ta kai ta dala biliyan biyar tsakaninta da Saudiyya.

A watan Mayu, gwamnatin tarayya da kuma Saudiyya sun amince da bunƙasa hulɗar kasuwanci da kuma ƙara yawan hannayen jari tsakaninsu.

Hakan ne ma ya sa wasu kamfanonin Saudiyyar kamar SALIC ke zuba jari a Najeriya, da nufin inganta harkokin kasuwanci da kuma na noma yadda ya kamata.

Dangane da haka ne Tinubu ya tabbatar wa masu zuba jarin daga Saudiyya cewa za a ba su cikakken goyon baya a yunkurinsu na zuba jari a ƙasar mai girman tattalin arziki a Afrika.

Kazalika, Saudiyyar ta bayyana aniyarta ta tallafa wa Najeriya kan harkar samar da ababen more rayuwa.

Ababen more rayuwa na da matukar alfanu musamman ganin yadda gwamnatoci ke ware maƙudan kuɗaɗe cikin kasafin kuɗi na kowace shekara domin gina tituna, da makamntansu domin sama wa jama’arsu walwala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *