Friday, December 5
Shadow

Ƴansandan sun kama mutumin da ake zargi da kashe tsohuwar matarsa

Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, ɗan shekara 40, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa Hadiza Sale, ƴar shekara 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara.

Wanda ake zargin ya shafe sama da makonni biyu yana ɓuya tun bayan da lamarin ya faru a ranar 10 ga Yuli, 2025.

Ana zargin mutumin da kashe matar ne ta yin amfani da sanda sa’ilin da take kan hanyar komawa gida bayan ta dawo daga kasuwa da daddare.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, kakakinta SP Shi’isu Lawan Adam ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga ofishin Aujara ne suka samu nasarar kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, 2025 a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani bayan tsantsan bibiyarsa da suka yi da kuma tura jami’ai na musamman don gano inda yake ɓuya.,

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Sabuwar Wakar Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da matar Rarara, Aishatulhumaira ta yi ta jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ta yaya ta yi waka da wanda ba mijinta ba?

Rundunar ta kuma sanar da cewa mutumin na hanunta, a sashen binciken laifuka da ke Dutse, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da shi gaban kotu.

1 Comment

Leave a Reply to YUNUS JAMES Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *