Tuesday, April 7
Shadow

Dan Allah ku gayawa El-Rufai ya shafa min Lafiya, Ni Aiki nane a gabana ba cece-kuce a gidajen watsa labarai ba>>Nuhu Ribadu

Ba Zan Yi Musayar Yawu Da Nasir El-Rufai Ba, Cewar Nuhu Ribadu

“An ja hankalina zuwa ga hirar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi da kafar yada labarai da yammacin ranar Litinin.

Da ba don gudun kada na yi shiru a gaskata maganganunsa ba, da na yi watsi da shi. Saboda na fi shagaltuwa da tarin aiyukan da ke gabana,fiye da tanka ire-iren su Nasir El-Rufai a kafafen yada labarai.

Duk da cin zarafi da aibata ni da Nasiru yake yi, hakan bai sa na taba fadin wani mummunan abu akansa ba a ko’ina. Ba don komai na ki aibata shi ba sai don mutunta zumuncin da ke tsakaninmu da kuma abotar mu ta baya, don haka abinda ban yi tun a baya ba, ba zan fara yanzu ba.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur ne saboda ci gaban Najeriya ba tare da damuwa ko za'a sake zabensa ba a 2027>>Inji Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila

Sai dai ina kira ga jama’a da su yi watsi da ikirarin El-rufai akaina

Bari na kankare muku shakku in fadi da babbar murya cewa ban taba tattauna batun ko zan yi takarar shugabancin kasa a shekarar 2031 da kowa ba, domin hankalina da gangar jikina sun ta’allaka ga aikina na ganin ci gaban Najeriya da nasarar gwamnatin shugaba Tinubu.

Don haka ina rokon Nasir El-Rufai da ya bar ni na ci gaba da fuskantar aikina na gina kasa kamar yadda ban dame kaina da al’amuransa ba”. Nuhu Ribadu

Me zaku ce ?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *