Saturday, March 15
Shadow

An kama Fasto da yin mu’ujizar karya inda yace ya mayar da wata mata me kudi amma sai bayan kwanaki aka ganta tana sayar da Lemun Kwalba

Wani fasto me suna Ebuka Obi ya shiga idon Duniya bayan da aka kamashi yana yiwa mabiyansa karya ta hanyar mu’ujizar karya.

Faston dai ya kai wata mata cocinsa me suna Zion Prayer Movement Outreach inda ta yi ikirarin cewa da tana da 300,000 amma data hadu da faston kudinta sun yi albarka har ta sayi gidan Miliyan 500 a Lekki jihar Legas.

Saidai kwanaki bayan yin wannan ikirari, An ga matar tana sayar da lemun Kwalba.

Matar dai har wani gida ta je ta nuna wanda tace nata ne amma daga baya me gidan sai da ya kamata akan ikirarin da ta yi na gidansa.

Karanta Wannan  Bidiyo: Tinubu da 'yan majalisa suna rera sabon taken Najeriya

A baya dai, Faston ya taba yin ikirarin warkar da marigayi dan fim din Kudu, John Okafor wanda aka fi sani da Mr. Ibu daga cutar dake damunsa amma kuma sai gashi daga baya dan fim din ya mutu.

Faston dai na ikirarin cewa shi annabi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *