Sunday, March 16
Shadow

Motar ‘yansanda ta kashe karamar yarinya a wajan bin me laifi

Motar ‘yansanda a jihar Legas ta kashe wata karamar yarinya me shekaru 6 a yayin da suke bin wani me laifi.

Lamarin ya farune a yankin Iyana Ipa dake birnin Legas.

Mahaifin yarinyar, Nnamdi Ugorji ya bayyanawa majiyarmu cewa, ‘yansanda daga ofishin ‘yansandan na Mosholashi ne suka biyo me laifi inda a haka ne suka buge diyarsa me shekaru 6 ta mutu.

Yace diyarsa da ‘yan uwanta sun je banki ne ciro kudi a kan hanyar ne motar ‘yansandan ta bugesu, yace kuma ‘yansandan sun so canjawa lamarin fasali inda suke nuna cewa motarsu ta yi kulikulin kuburane.

Yayi kira ga shugaban ‘yansanda da shugaban kasa da ministar mata da su tabbatar wanda suka aikata wannan lamari an hukuntasu.

Karanta Wannan  Abin a Yaba: Ya tsinki Dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ya mayarwa mesu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *