Monday, December 16
Shadow

Hotunan mata 2 da suka fito takarar shugaban kasa a kasar Iran

Mata biyu ne suka fito takarar shugaban kasa a kasar Iran biyo bayan rasuwar tsohon shugaban kasar, Ebrahim Raisi a hadarin jirgin sama me saukar Angulu.

Mace ta farko itace Zohre Elahian wadda ‘yar majalisar tarayyar kasar ce kuma tana da karatu har zuwa digiri na 3 watau(Doctorate) a fannin physics.

Sai kuma mace ta biyu me suna, Hamideh Zarabadi wadda itama ‘yar majalisar tarayyar kasar ce kuma tana da digiri na 3 watau( Doctorate) a fannin engineering.

Saidai kasancewar Iran kasar Musulmi ce da take riko da addinin musulunci sosai da kamar wuya su yadda su zabi mace a matsayin shugaban kasa.

Karanta Wannan  Kalli Yanda sojojin kasar Yahudawan Isàèlà ke taka tutar kasar Saudiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *