Friday, September 11
Shadow

Har yanzu muna nan kan Bakanmu cewa, Tinubu ya sabawa doka dakatarwar da yawa Gwamnan jihar Rivers kuma muna kiran ya dawo dashi>>Kungiyar Lauyiyi ta Najeriya, NBA

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA ta bayyana cewa har yanzu tana nan kan bakanta dake cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sabawa doka dakatarwar da yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.

Shugaban kungiyar, Afam Osigwe ne ya bayyana haka a wata hitmra da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

Ya bayyana cewa, suna kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dawo da Gwamna Simi Fubara akan mukaminsa.

Yace gwamnan rikon kwarya da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada ba bisa doka aka nadashi ba dan haka su basu yadda dashi ba.

Karanta Wannan  Yanzu haka ina wani Kess: Ango ne yayi aure amma ya kasa shiga dakin amaryarsa saboda an tura masa Bidiyon ta wani na mu'amala da ita>>Inji Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *