
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga watan October me zuwa zata fara baiwa daliban Najeriya kyautar data ta 100MB.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis.
Ministan yace zasu hada kai da hukumar sadarwa ta kasa, NCC da tabbatar da wannan shiri nasu.
Yace za’a fara da daliban sakandare dana jami’a ne kamin a fadada shirin daga baya.
Yace sun dauki wannan matakine dan saukakawa daliban shiga shafukan kara Ilimi kyauta da kuma ragewa daliban radadin tsadar data.