Friday, September 11
Shadow

Kalli Bidiyon: Matar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Watau Remi tace bata taba zuwa jihar Zamfara ba

Matar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu watau Remi tace ta zagaye jihohin Najeriya kaf amma banda jihar Zamfara.

Ta bayyana hakane a jihar Imo yayin wani taron siyasa.

Tace amma nan gaba tana son zata je jihar Zamfara inda ta karfafawa sauran mutanen Najeriya su rika zagayawa dan su san sauran ‘yan uwansu ‘yan Najeriya.

Ta kuma bayyana cewa ita a makarantar sakandare, Abokanta na gaya mata cewa, tana kama da inyamurai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Wani Fasto da yace ya gaji da wa'azi, ya koma Boka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *