Thursday, August 20
Shadow

In ka ga dama ka tara duka Gwamnonin Najeriya a APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabenka dole ka sauka>>El-Rufai ga Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mayar da martani kan yanda Gwamnoni ke rububin komawa jam’iyyar APC.

El-Rufai yace idan gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ga dama, ta tara duka ‘yan Adawa a jam’iyyar APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabensa dole ya sauka.

El-Rufai yace kuma hadakar da suke ta ‘yan Adawa tsaf cikin sauki zasu iya kawar da gwamnatin Tinubu ba tare da Gwamna ko daya ba.

El-Rufai ya bayyana hakane yayin ganawa da ‘yan Jarida a Kano, ranar litinin inda yace Idan Tinubu ya ga dama ya tara duka Gwamnonin Najeriya a APC amma idan ‘yan Najeriya suka ki zabarsa shikenan ta kare.

Karanta Wannan  Da Sheikh Dr. Ahmad Gumi, watau Abdulrahaman Ahmad ya kammala ya kammala makarantar horas da sojoji ta NDA

A jiyane dai APC ta karbi gwamnan jihar Delta daya canja sheka daga PDP.

Hakanan Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace akwai karin gwamnoni da zasu koma jam’iyyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *