Friday, December 12
Shadow

Zaki ya kàshè me gidansa balarabe ya kuma cinye gawar kwanaki kadan bayan da ya siyoshi ya rika wasa dashi a gida

Wani zaki da Balarabe a garin Najaf dake kudancin kasar Iraqi ya siyo dan ya rika wasa dashi, ya kashe me gidan nasa kwanki kadan bayan siyoshi.

Bayan ya kasheshi, ya kuma cinye kusan duka gawar me gidan nasa.

Lamarin ya faru ranar 8 ga watan Mayu.

Kakakin ‘yansandan yankin Najab, Mufid Tahir, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sai da aka kashe zakin saboda yaki yadda ya daina cin gawar me gidan nasa.

Me gidan Aqil Fakhr al-Din na da shekaru 50 kuma an bayyana cewa ya dade yana ajiye zaki a gidansa.

Karanta Wannan  Furuciñ Da Na Yì Na Cewa Koda Añnàbì SAW Źaì Hana Maùludì Ni Sai Na Yi, Tabbas Ña Yi Kusķùrè Kuma Ina Rokon Alĺah Ya Yafe Mìn, Cewar Mawakin Yabo, Hafiz Abdallah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *