Friday, December 5
Shadow

A mulkin Tinubunnan nima yunwa ta kamani>>Inji Rotimi Amaechi

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, Yunwa ta kamashi.

Amaechi ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwarsa.

Yace Dukkan mu nan muma cikin yunwa, idan baku ciki ni ina cikin yunwa.

Amaechi yace duk da yana APC amma bai zabi Tinubu ba a matsayin shugaban kasa ba.

Amaechi dai shine yazo na 2 a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2022 wanda Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaben.

Yace idan suka dage a matsayinsu na ‘yan Adawa zasu iya kwace mulki daga hannun Tinubu.

Karanta Wannan  Ta yiwa Dangin Tsohon Mijinta Gargadin kada su rabata da Diyarta a Tiktok, saidai da yawa na tambayar Dangin Tsohon Mijin nata na yin Tiktok ne?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *