Friday, December 5
Shadow

Bazan iya zama jam’iyya daya da El-Rufai ba, saboda bashi da akida>>Inji Sanata Wadada yace ya bar jam’iyyar SDP

Sanata Ahmed Aliyu Wadada daga Jihar Nasarawa ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar SDP.

Ya bayyana cewa dalilinsa na barin jam’iyyar shine ba zai iya ci gaba da zama da wadanda basu da akida a jam’iyya daya ba.

Ya bayyana hakanne a hirarsa da ‘yan jarida inda yace Musamman Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, yace bashi da akida.

Yace El-Rufai na kan gaba wajan jawo hankalin mutane da cewa ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya.

Ya kara da cewa shine ya ce a zabi Tinubu amma saboda bai samu mukamin Minista ba amma ya bar jam’iyyar.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan 23.35 daga Kuwait dan ta yi maganin matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *