
Wannan wasu jami’an tsaro ne, daya sojan ne dayan kuma jami’in hukumar kula da gidajen gyaran hali ne da aka kama bisa zargin fashi da makami.
Dukansu sun amsa laifukan da ake zarginsu.
An dai gansu cikin shigar kayan sojoji.
Da yawa dai sun bayyana su a matsayin maciya amanar kasa.