Friday, December 5
Shadow

A karin farko: Kasashen Canada,UK, Australia da New Zealand zasu kakabawa kasar Israyla takunkumi saboda kìsàn Kiyashin da sukewa Falasdiynawa

Kasashen Canada,UK, Australia da New Zealand zasu kakabawa wasu jami’an Gwamnatin kasar Israela 2 takunkumi.

Wadanda za’a kakabawa wannan takunkumi sune Itamar Ben Gvir da Betzalel Smotrich wanda ‘yan siyasa ne masu rura wutar ci gaba da kisan Falasdiynawa.

Rahotanni a baya sun ce duka kasashe masu fada a ji na Duniya sun amince a dakatar da yakin Gaza in banda kasar Amurka.

Dubban mutane ciki hadda mata da kananan yara ne aka kashe a Gàzà wanda kasashen Duniya ke cewa an aikata laifukan yaki.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya taya Tsohon Shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar murnar cika shekaru 83

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *