
Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan Adam na DSTV sun sanar da rage farashin da ake biya dan kallo duk wata daga Naira dubu 20 zuwa Naira Dubu 10.
Hakan na zuwane bayan da kamfanin ya tafka asarar miliyoyin kudade saboda da yawan ‘yan Najeriya sun daina saka kudi dan kallon.
Saidai abin jira a gani shine ko hakan zai sa mutane a yanzu su dawo su ci gaba da biyan kudi dan kallon DSTV din?