Friday, December 5
Shadow

Tinubu Ya Naɗa Tsohon Hadimin Buhari Shugaban PCNGi

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ismael Ahmed, tsohon hadimin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayin Shugaban Hukumar Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGi). Wannan shiri na gwamnati na da nufin rage radadin cire tallafin fetur ta hanyar samar da makamashi mai araha da tsafta.

Ismael Ahmed ya kasance mai ba Buhari shawara kan Shirin Tallafin Jama’a tsakanin 2018 zuwa 2022. Ya kammala karatunsa na lauya a Jami’ar Abuja, sannan ya samu digirin digirgir a fannin Hulɗar Ƙasashen Duniya daga Jami’ar Webster da ke Amurka.

Karanta Wannan  A yayin da Gobarar California kasar Amurka ke ci gaba da yaduwa, an hango wata mahaukaciyar Guguwa ta taho zata rura wutar ta kara shiga cikin gari dan ci gaba da kona gidaje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *