Friday, December 5
Shadow

NAHCON ta kammala jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya

Hukumar Alhazan Najeriya ta kamala jigilar alhazan ƙasar da suka sauke farali a aikin hajjin bana.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kammala aikin kwaso alhazan daga ƙasa mai tsarki a yau Laraba 2 ga watan Yulin 2025.

Kimanin alhazan Najeriya 41,291 ne suka sauke farali a wanan shekara, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Jirgin ƙarshe da ya ɗauko alhazan jihar Kaduna ya taso da safiyar yau.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Tauraruwar fina-finan Hausa, Khadija Osi ta sake daukar hankula bayan sakin wannan zazzafan Bidiyon tana rawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *