
Tauraron Tiktok daga kasar Nijar, Hassan Make-Up ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya sun bashi kunya kan murnar da suka rika yi ta rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Yace wane irin abune wannan?
Hassan Make-Up yace mahaukaci ne kadai zai rika murna da mutuwar wani.
Mutane da yawa ne suka fita kan titi suna murnar rasuwar Buhari.