
Dan gidan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB me suna Muhammad Babangida yace ya amince da mukamin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nadashi.
Ya musanta rahotannin dake cewa bai amince da nadin mukamin ba.
A ranar 18 ga watan Yuli ne shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada Muhammad Babangida mukamin shugaban bankin Noma BAO.
A sanarwar da ya fitar, me taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkar sada zumunta, Dada Olusegun yace Muhammad Babangida ya fitar da sanarwa a yau Litinin inda yace ya amince da mukamin da shugaba Tinubu ya nadashi.
Muhammad Babangida yace masu cewa wai bai amince ba na son bata gwamnatin Tinubu ne kawai.