
Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Flato na bayyana cewa, an barke da murna bayan da aka tabbatar da Professor Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC.
A yau ne dai aka bayyana Professor Nentawe Yilwatda a matsayin shugaban APC wanda ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.