Friday, December 5
Shadow

NNPCL ya musanta sayar da matatar mai ta Fatakwal

Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya musanta raɗe-raɗin sayar da matatar mai ta birnin Fatakwal.

Shugaban kamfanin Bashiru Ojulari ne ya bayyana haka a wani taron tuntuɓa da kamfanin ya shirya a shalkwatarsa da ke Abuja.

Ojulari ya ce NNPCL ba shi da aniyar sayar da wata matata mallakinta, sai dai ma ƙoƙarin gyara su domin yin daidai da zamani.

An fara raɗe-raɗin sayar da matatar ne bayan wata hira da shugaban kamfanin ya yi a taron OPEC a birnin Vienna na ƙasar Austria a farkon watannan.

A lokacin Ojulari ya yi wata hira da jaridar Bloomberg, kan batun sayar da matatar inda ya ce “komai zai iya faruwa”.

Karanta Wannan  Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan kasar China bisa zargin taimaka wa ƴan ta’adda

Tun daga wancan lokacin ne aka yi ta maganganu game da makomar matatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *