Thursday, February 5
Shadow

ADC ba barazana bane: Cikin Sauki Tinubu zai samu kuri’u Miliyan 15 a zaben 2027 ya lashe zabe>>Inji wani na hannun damar shugaban kasar

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Nicolas Felix ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai samu kuri’u Miliyan 15 a zaben 2027.

Yace wannan babu tantama akai.

Ya bayyana hakane a yayin da ya rabawa wasu mabukata man fetur kyauta a Suleja dake jihar Naija ranar Alhamis.

Ya ce Hadakar ‘yan Adawa a ADC ba zata zamarwa Shugaba Bola Ahmad Tinubu barazana ba.

Ya kara da cewa, kamar yanda ‘yan Adawar suka taho suka hadu, haka kuma zasu watse.

Karanta Wannan  YANZU YANZU: Wata kungiyar Matasan Arewa Masu goyon Bayan Bola Tinubu Wadda take da yawan Mabiya miliyan 100 ta yiwa Shugaban ƙasa Bola Tinubu Alƙawarin kawo Masa Miliyoyin kuri'un Matasan Arewa a kakar zaɓe Mai zuwa ta 2027

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *