
Rahotanni sun bayyana cewa, yajin aikin da malaman Jinya na Asibiti, watau Nurse suka shiga a karkashin kungiyarsu me suna (NANNM) ya zo karshe.
Ministan Lafiya, Professor Ali Pate ne ya bayyana hakan bayan ganawa da wakilan malaman jihar, Nurse a ranar Juma’a.
Saidai wakilan malaman jinyar sun ki cewa uffan bayan kammala zaman.
A baya dai malaman jinyar sun shiga yajin aikin kwanaki 7 na gargadi.