Friday, December 5
Shadow

PDP na shirin baiwa Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a shekarar 2027, ji bayani

Wani batu da ke jan hankali a siyasar Najeriya shi ne yadda bayanai ke cewa babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta na lallaɓa tsohon shugaban ƙasar GoodLuck Jonathan domin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027

Mista Jonathan ya ja baya a harkokin siyasa tun da ya fadi zabe a 2015, kuma jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da shi domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa don kalubalanar shugaba Bola Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Wasu masana na ganin cewa wannan mataki ne na gurgunta tafiyar haɗakar wasu manyan yan’awar ƙasar.

Majiyoyin sun shaida wa BBC cewa jam’iyyar ta PDP a hukumance, da kuma a matakin wasu jiga jigan ta, ciki har da gwamnoni ne ke wannan yunkuri na zawarto tsohon shugaban Najeriyar Good Luck Ebele Jonathan dominn ba shi takara a jama’iyyar a zaben 2027.

Malam Ibrahim Abdullahi, shine mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ta PDP, ya kuma tabbatar da wannan yunƙuri yana mai cewa tsohon shugaban Najeriyan ya nuna yiyuwar amincewa da wannan buƙata.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Karon Farko Nijeriya Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani

Ya ce yunƙurin nasu na bai wa Jonathan takara amsa kiran da ƴan Najeriya suka yi masu ne na dawowa da tsohon shugaban ƙasan saboda a yanzu an yi walƙiya kuma jama’a fahimci kuskuren da suka tafka a baya na ƙin zaɓen Jonathan.

”Abubuwan da shi wannan bawan Allah ya yi a lokacin da ya ke mulki shiyasa muke ganin babu laifi, tunda yana PDP har yanzu to a sake nemo shi, tunda ƴan Najeriya sun fahimci abubuwan da suka faru baya ba laifin shi bane har suna bashi haƙuri cewa don Allah ya zo ya cece su, kuma sun gane cewa mutum ne mai tausayi.

”Mu kuma da yake muna biyayya ne ga ƴan Najeriyan kuma su muke son mu kyautata wa, sai muka ga ya kamata abin da suke kira muma mun saurare shi kuma an y kira gare shi,” In ji Malam Ibrahim Abdullahi.

Karanta Wannan  Ku kawo mana rahoton duk wanda bashi da aikin yi amma yake rayuwar kece raini>>Inji Ministan tsaro,Bello Matawalle

Baya ga tabbacin wannan batu da BBC ta samu daga mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ta PDP, wata majiyar ta daban ta bayyana yadda a baya bayan nan wasu jiga jigan jama’iyyar suka bi Mista Jonathan har ƙasar Gambia a makon da ya gabata, duk dai domin neman shawo kansa ya yi masu takara.

Kawo yanzu dai, Malam Ibrahim Abdullahi, ya ce tsohon shugaban Najeriyan ya nuna alamun amincewa da wannan buƙata ta su, harma ya gindaya wasu sharuɗɗa.

Ya ce ”Ya fara sauraron mutanen kuma ya fara bayar da sharuɗɗa da suka shafi ko za a haɗa shi takarar sharar fage tare da wasu, ko kuma da gasken ake an fahimci ingancin shi na tsayawa zaɓe da kuma tuntuɓar masu bashi shawara.”

A nasu ɓangaren, masana harkokin siyasa a Najeriya, irin su Farfesa Abubakar Kari na jami’ar Abuja na ganin cewa irin wannan alamu ne cewa za a yi karan batta a zaɓen 2027.

Karanta Wannan  Matar shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan Dari bakwai wajan yawon zuwa kasashen Duniya a cikin watanni 3 kacal

Ya ce ”Idan har Goodluck ya yi takara kamar ya sake fesa rai ne ga jam’iyyar PDP wadda ga dukkan alamu ta yi doguwar suma. Haka nan kuma ina ganin takarar Goodluck Jonathan za ta zamo cikas ga masu yunƙurin yin haɗaka saboda har zuwa yanzu su ne suke tunanin cewa za su zama tunga ta adawa.”

Akwai kuma wasu rahotannin na daban da ke cewa wasu jagororin jama’iyyar hamayyar ta PDP suna ta ganawa da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin zawarcin shi zuwa jama’iyyar, don ya yi takarar tare da Jonathan a matsayin mataimaki.

Wannan dambarwa dai na faruwa ne a yayin da ake ta shirye shiryen tunkarar zaɓen 2027 da mutane da dama ke ganin zai zamo daya tamkar da dubu a zaɓukan Najeriya.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *