
Tsohon Gwamnan Jigawa, Malam Sule Lamido yace masu son zama shugaban kasa, sun yi yawa a jam’iyyar ADC.
Sule Lamido ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Sule Lamido wanda yana daga cikin wadanda suka halarci taron farko na hadakar ‘yan Adawa da suka zabi APC a matsayin jam’iyyar su, yace ba zai bar PDP zuwa karamar jam’iyya ba.
Yace yana baiwa masu son shugabanci a jam’iyyar ta ADC dasu natsu su zama cewa sun samu alkibla da hafin kai.
Akwai Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da duka suka bayyana son tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta ADC.