Thursday, February 5
Shadow

Idan PDP ta yi nasarar shawo kan tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara a 2027, babu wanda zai iya kayar dashi>>Sule Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya fi dacewa da zama ɗan takarar jam’iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2027, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su yi duk mai yiwuwa wajen jawo hankalin tsohon shugaban a kan ya koma jam’iyyar ya tsaya takara.

“Ina tunanin ya kamata PDP ta janyo shi: shi ne ya fi dacewa ya mata takara. Duk wani ɗantakara da PDP za ta tsayar, ƴan Najeriya za su zaɓe shi,” in ji tsohon gwamnan kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da tashar Channels.

Lamido ya bayyana Jonathan a matsayin wanda ya fahimci ƙasar kasancewar ya yi mulki a baya, kuma ya san yadda zai yi mu’amalanci mulkin ƙasar.

Karanta Wannan  Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam'iyya butulci ne - Kwankwaso

Ya ce ba su da wani ɗantakara daga kudancin Najeriya da ya fi tsohon shugaban ƙasar idan ana batun wanda za su tsayar a zaɓen wanda ke tafe.

“Ni dai a nawa tunanin, duk da cewa ba wai ina raina sauran ƴan jam’iyyarmu ba ne, amma lallai Jonathan ne ya fi dacewa da yin takara a PDP.”

Wannan jawabin na Lamido na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da yaɗa raɗe-raɗin cewa Jonathan zi tsaya takara a zaɓen mai zuwa domin fafatawa da Bola Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *