Friday, December 5
Shadow

Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina.

Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da bayar da alawus-alawus ga Limaman Coci a matsayin wani ƙoƙari na haɗin kai a addinai da kuma bayar da gudummawa ga Malaman addinai.

Ƙungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Katsina ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da sakataren Kungiyar Dakta Musa Daniel Danladi ya fitar a madadin Shugaban Ƙungiyar Very Rev. Fr. Richard Shuaibu Liti.

Haka zalika, yace Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya amince da ɗaukar Malaman da suka karanci addinin kiristanci domin karantarwa a makarantun gwamnati, inda Kungiyar CAN ta bayyana cewa hakan zai tabbatar da daidaito da ci gaba, tana mai cewa ƙungiyar ta daɗe tana neman haka.

Karanta Wannan  Bayani Dalla-Dalla: Karanta Kabakin Alherin da Gwamnatin tarayya zata rikawa iyalin Buhari, Za'a rika biyan A'isha Buhari Naira Dubu dari uku da hamsin duk wata amma daga ranar data sake yin aure shikenan za'a daina biyanta, Ji sauran Abubuwan da za'a musu

Usman Salisu, Daga kafar Katsina Daily News

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *