
Dan majalisar wakilai na majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude ya nada masu taimaka masa guda 106.
Ya bayyana hakane a hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace ya nada mutane 106 a matsayin masu taimaka masa ne dan ya tallafawa rayuwarsu.
Yace daga ciki akwai wadanda yake biya albashin Naira Dubu 10 har zuwa Dubu 100.
Dan majalisar wanda a jam’iyyar SDP yake daga mazabar Uke/Karshi yace ya tallafawa mutane a bangarori daban-daban da suka hada da Noma, ilimi, da sauransu.