
An samu suka ga bankin Ja’iz wanda na Musulunci ne saboda kin aikawa masu hulda dashi sakon taya murnar Maulidi.
Wani da yayi korafi akan hakan yace abin takaici shine bankunan da bana Musulunci ba sun aikawa musulmai sakon taya Murnar maulidi.
Amma bankin na Ja’iz wanda yake ikirarin na musulmai ne be aika sakon taya murnar maulidi ba.
Wasu dai sun yi barazanar daina hulda da bankin na Ja’iz.
Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad shima ya tabbatar da hakan inda yace shima ya lura bankin na Ja’iz basu tura sakon taya Maulidi ba.
Wasu dai na alakanta bankin da cewa ba Izala ne shiyasa hakan ta faru.
Gaskiya dai abun akwai abun dubawa