
Wannan matashiyar dalibar aji daya a jami’ar jihar Nasarawa me suna Comfort Jimtop Oliver ta rigamu gidan gaskiya a dakin Saurayinta.
Tuni dai aka dauke gawarta zuwa mutuware dan fara binciken dalilin mutuwarta.
An tuntubi hukumar makarantar kan lamarin amma bata ce komai ba tukunna.
Amma wasu daga cikin makarantar sun tabbatar da faruwar lamatin.
Kakakin ‘yansandan jihar, James Lashen ya tabbatar da faruwar lamarin.