
Bidiyon ganawar tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a Kaduna wajan daurin auren dan Sanata Abdulaziz Yari ya dauki hankula sosai.
A Bidiyon an ga yanda shugaba Tinubu ya mike tsaye suka gaisa da Sule Lamido, da yawa sun rika cewa, siyasa ba da gaba ba.