
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na shirin komawa jam’iyyar ADC.
Wasu majiyoyi ne suka fadawa kafar Punchng hakan a asirce daga jam’iyyar ADC din saboda basu da ikon yin magana da yawun jam’iyyar.
An jima dai ana rade-radin cewa, tsohon shugaban kasar zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 amma shi bai fito ya tabbatar da hakan a hukumance ba.