
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana sane da irin halin matsin rayuwar da ake ciki.
Saidai yace abin ya kusa zuwa karshe dan kwanannan lamura zasu gyaru sosai.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron makamashi da aka gudanar a Abuja ranar Talata
‘Yan Najeriya da yawane ke kokawa da matsin rayuwa tun bayan hawan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Mulki a shakarar 2023.