
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa babu dan siyasar da zai iya kayar da shugaban kasar daga mulki a zaben shekarar 2027.
Me baiwa shugaban kasar shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin ganawa da wasu kungiyoyin goyon bayan shugaba Tinubu su 100.
Ya bayyana cewa, shugaba Tinubu ya kafu sosai a kowane sashi na kasarnan babu wanda zai iya kayar dashi zabe.