
Rahotanni daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria jihar Kaduna sun musanta labaran dake cewa jami’ar na kera makamin kare dangi.
Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Awwal Umar ne ya bayyana haka inda yace babu kanshin gaskiya a Bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta.
Bidiyo dai ya rika yawo a kafafen sada zumunta inda aka rika cewa, Jami’ar ta ABU na kera makamin kare dangi bisa hadin kan kasar Pakistan.
Saidai jami’ar ta fito ta musanta wannan ikirari.